Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka

Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar

Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania.

Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II.

A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta Nato ba.

Shugaban yace EU zata gaggauta tattarawa harkokin tsaron kasashen EU saboda bunkatashi da sauri.

De Leyen ya kara da cewa ba zai yu a tattauna dangane da yakin a Ukraine ba tare da ita kasar Ukraine ko kasashen turai ba. Kasashen kungiyar 26 daga cikin 27 sun amince da wannan matin da suka fara dauka in banda kasar Hungary.

Volodomir Zelesky na kasar Ukraine ya isa taron kafin a fara shi a birnin Brssels, ya kuma godewa kasashen na Turai kan wannan kokarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments