Shugaban kasar Amurka ya ci gaba da fadin kalamai na zagi ga tsohon mai taimaka masa a harkokin gwamnati bayan sun babe.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana cewa hamshaken attajirin ya haukace.
Labarin ya nakalto Fadar white house na karyata zancen cewa mutanen biyu zasu dinke barakan da ta faru a tsakaninsu wanda yasa shugaban ya kore shi. Wani mai Magana da yawun fadar white House yana cewa shugaban bai da wani shin a Magana da Musk a yau.
Ya ce Trump ba ya kaunar sake ganinsa, duk da cewa Musk ya bayyana anniyarsa ta gyaran barakar da ta barke a tsakaninsa da maigidansa shugaba Trump.
A safiyar jiya Jumma’a Trump ya fadawa radiyon ABC kan cewa bai son ganin Musk kuma ballanta na ya zanta da shi.
Kafin haka dai Musk ya ce Trump bai da godiya, kuma ya nuna butulci , don ba zai lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar da ta gabata ba idan bas hi ba. Don haka shi ya sa shi a fadar white House.