Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya Sanya hannu a kasafin kudi na shekara mai zuwa wato 2025, wanda banaren tsaro ya sami kaso mafi tsoka na kashi 32.5 %.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan shi ne kasafin kudi mafi tsoka da shugaban ya warewa bangaren tsaro a tarihin kasar Rasha na baya bayan nan.
Kafin haka dai majalisun dokokin kasar Rasha guda 2 sun rika sun amince da kasafin kudin na shekara mai zuwa, wato kwanaki 10 da suka gabata. Bangaren tsaron dai ya sami dalar Amurka biliyon $126 wato (Rubles Biliyon 13.5) wanda kuma shi ne kashi 32.5% na dukkan kasashen kudin.
Putin ya sanyawa wannan kasashen kudi hannu ne a dai lokacinda wasu manyan-manyan jami’an tarayyar Turai suke ziyara a birnin Kiev don nuna goyon bayansu gareta.
Zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump dai yace zai kawo karshen yakin Ukraine da Rasha idan ya karbi shugabancin kasar Amurka. Saboda baya son Amurka ta ci gaba da kashe kudade a yakin. Don haka idan an dakatar da yaki a Ukraine, wannan ya nuna cewa Rasha ta sami nasara a yakin don tana iko da yankunan da ta mamaye a Ukraine kenan a shekara ta 2022.