Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72

Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan

Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai kamawa.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja ya na fadar haka a wani taro baje kolin hotunan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II.

Andrey Podelyshev ya ce idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki, ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan Rasha, to zata rama da hare-hare masu tsanani.

Shugaban Volodimir Zelesky na kasar Ukraine tuni ya yi watsi da tsagaita wutar ya kuma kara da cewa Rasha tana son ta ja hankalin duniya ne, da wannan tsagaita wuta, don amfanin kanta a yakin da suke fafatawa. A halin yanzu dai an dau kwanaki kimani 1,159 ana fafatawa tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments