A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi.
Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin wakilan majalisun, kasashe mambobi.
An bude taron ne dai daga jiya Talata 13 ga watan Mayu, zai kuma ci gaba har zuwa ranar 15 gare shi.
Tun a jiya ne dai wakilan Iran su 4 daga majalisar shawarar musulunci ta kasar su ka isa birnin na Jakarta domin halartar taron.