Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Taron Kungiyar BRICS Zai Kawo Bunkasar Tattalin Arziki

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Taron kungiyar BRICS wata dama ce ta bunkasa alaka mai karfi ta tattalin arzikin duniya Shugaban

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Taron kungiyar BRICS wata dama ce ta bunkasa alaka mai karfi ta tattalin arzikin duniya

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Halartar tawagar wakilan majalisar dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a zauren majalisar dokokin BRICS wata dama ce mai kima ta bunkasa alaka da kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da kuma fuskantar takunkumi.

A wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Asabar kafin ya tashi zuwa wasu kasashen Latin Amurka uku da kuma halartar taron majalisar dokokin kasashen kungiyar BRICS, Qalibaf ya ce: Za su zagaya kasashen Latin Amurka, inda zasu fara da kasar Venezuela, bisa gayyatar da shugaban majalisar dokokin kasar ya yi masa, domin karfafa alaka a fannonin tattalin arziki, siyasa, da al’adu.

Haka nan kuma yayi nuni da kebantattun kyawawan halayen kasashen Latin Amurka, yana mai bayyana cewa: Wannan yanki mai yawan al’umma sama da miliyan 600, yana da kyakkyawar alaka da Iran a fagen kasa da kasa, kuma dukkaninsu suna yin Allah wadai da daukan matakin bangare guda, kuma suna goyon bayan bangaren hadin kai. Wannan ya ba da dama mai kyau na bunkasa alakarsu da Jamhuriyar Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments