Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta taimaka wa Lebanon wajen dakatar da fuskantar zalunci da wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya
Shugaban Majalisar Dokokin kasar Lebanon Nabih Berri, ya jinjinawa irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take baiwa gwamnati da al’ummar kasar Lebanon da kuma gwagwarmaya, inda ya bayyana cewa Iran tana taka muhimmiyar rawa a fagen bayar da taimako ba tare da wani sharadi ba ga kasar Lebanon. Tare da jaddada cewa akwai wani dodo da ake kira da gwamnatin ‘yan sahayoniyya, da taimakon Iran suka samu damar dakatar da wannan muguwar dabbar.
A yayin tattaunawarsa ta hanyar wayar tarho da Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf, a jiya Asabar, Nabih Berri ya yaba da matsayin takwaransa na Iran wajen nuna goyon baya ga kasar Lebanon, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta taka muhimmiyar rawa a fagen bayar da taimako ba tare da wani sharadi ba ga Lebanon. Yana mai jaddada cewa akwai wani dodo da ake kira gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ke kokarin ruguza yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.
Berri ya kara da cewa: Da taimakon Iran suka sami damar dakatar da wannan babban dabbar daji, yana mai jaddada cewa kudancin Lebanon, yankunan Bekaa da kuma yankunan kudancin kasar suna cikin yanayi mai kyau a halin yanzu.