Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara.
Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom.
Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’.
Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JMI. Yace tunanin Imam Khumaini Q ne ya taiamakawa mutanen kasar Lwabanon suka kai inada suka kai. Kuma alkawalin All…Gaskiya ce, nasara tana zuwa ga musulmin yankin da kuma duniya gaba daya.