Shugaban Kungiyar Hizbulla Ya Ce Kungiyarsa Ba Zata Taba Mika Kai Ga Bukatun HKI Ba

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa gwamnatin kasar Lebanon don kawo karshen kungiyar ba.

Tashar talabijin ta Almanar ta kuma kungiyar ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya litinin, a wani jawabinda ya gabatar ta tashar don tunawa da shahadar babban kwamandar kungiyar Sayyed Mustafa Badreddin wanda yayi shahada shekaru 9 da suka gabata.

Sheikh Kasim ya kara da cewa kungiyar tana kan al-kawalinta na tsagaita budewa juna wuta duk tare da cewa HKI ta keta wannan yarjeniyar har sau kimani 3000.

HKI dai ta amince da tsagaita budewa juna wuta ne bayan fafatawa da kungiyar Hizbullah na tsawon watanni 14, a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kudancin kasar Lebanon.

Sannan bayan ta rasa daruruwan sojojinta a kan iyakar kasar Lebanon wadanda suka dauki kimani watannin 2 suna kokarin shiga kasar ta Lebanon daga kudancin kasar tare da tankunan yakin Mirkava,  amma suka kasa yin hakan.

Sheikh Kasin ya bayyana cewa dukkan kokarin HKI da Amurka na shafe al-ummar Falasdinawa a Gaza ko a yankin yamma da kogin Jordan ba zai kai ga nasara ba. Duk da cewa manufarsu ta shafe kasar Falasdinu daga doron kasa ne fiye da shekaru 75 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments