Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace

Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya

Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk suna cikin irin tallafin da kasar Iran tayiwa Falasdinawa.

Khalila Al-Hay  ya kuma kara da cewa, shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump da kuma Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu na kwace Gaza daga hannun  Falasdinawa, ba zai gai ga nasara ba.

Yace Saboda mutanen Gaza, suna goyon bayan kungiyar Hamas a duk tsawon watanni 15 da mayakan kungiyar suka fafata da sojojin HKI da Amurka. Ya kara da cewa ko da za’a sake wani yakin Tufanul Aksa, mutanen Gaza suna tare da kungiyar Hamas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments