Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa a kafafen yada labarai na masu gwagwarmaya.
Ya kuma kara da cewa a halin yanzu yakamata mutanen kasar su maida hankali wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma dogaro da kai kan dukkan abubuwan da yakamata ba zasu nemi shi nan gaba daga wajen makiya ba.
Mutanen kasar Yemen karkashin kungiyar dai ta yaki kasar Saudiya da kawayenta na tsawon shekaru 8 ba tare da sun sami nasara a kanta ba, haka ma ta shiga yaki na watanni 15 da HKI da MAurka da kuma Burtania, a matsayin tallafi ga mutanen Gaza a kasar Falasdinu da aka mamaye. Inda kasar ta sami nasara a cikin dukkan wadannan yake-yaken.