Shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro ya bayyana shugaba Shahid Ibrahin Ra’isi a matsayin dan’uwansa kuma abokin gwagwarmaya don neman yenci a wannan zamanin.
Shafin yanar gizo na ‘Arrasalah’ ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake zantawa da mukaddashin shugaban kasar Iran Muhammad Mukhbir a yau laraba, ya kuma kara da cewa, mutanen Venezuela ba zasu taba manta da shugaba Ra’isi ba saboda yadda kasashen biyu suka kusanci juna a lokacin shugabancinsa.
Madoros ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Imam Sayyid aliyul Khaminaee jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran da kuma sauran mutanen kasar Iran kan wannan rashin.
Shugaban kasar Venezuela ya kamala da cewa yana da yakini, alkwai alkhairi mai yawa a gaban kasar Iran, kamar yadda aka saba da samun kasashen wadanda suke gwagwarmaya don neman yenci a tarihin duniya.