Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimmancin kara inganta taimakekkeniya a tsakanin kasashensu.
Shugaban na Iran ya fada a yammacin yau Laraba cewa: Ci gaba da tarukan tsakanin jami’an kasashen biyu ke yi na tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai jaddada karfafa alaka da kasashe makwabta, musamman kasar Qatar, a matsayin wani muhimmin ka’ida na manufofin ketare na Iran.
Shugaban kasar ya ci gaba da cewa: Sun tattauna da Sarkin Qatar kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu ta hanyar da za ta tabbatar da moriyar kasashensu, kuma an yanke wasu muhimman shawarwari na raya kasa da zurfafa dangantaka da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Sarkin Qatar ya kuma jaddada bukatar samar da sabbin damar gudanar da hadin gwiwa.
Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kasashen yankin suna da karfin daukar matakai na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, bisa tushen kyakkyawar makwabtaka da mutunta juna da kyautata mu’amala mai ma’ana, da share fagen kafa wani tsari na hadin gwiwa da taimakekkeniya.