Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Kare Alkawuran Da Ta Dauka

Shugaban kasar Iran ya jaddada matakin kasarsa na mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka kulla da kasashen Turai amma Amurka ta fice daga ciki domin kara

Shugaban kasar Iran ya jaddada matakin kasarsa na mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka kulla da kasashen Turai amma Amurka ta fice daga ciki domin kara dagula al’amura

A ganawarsa da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi da yake ziyarar aiki a kasar Iran, shugaban kasar Iran Masaud Pezeskian ya yi ishara da yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla tsakanin kasarsa da Amurka da kasashen Turai, kuma bisa tabbatattun rahotannin da dama daga hukumomin kasa da kasa, Iran tana  aiwatar da dukkan wajibcin da suka rataya a wuyanta a karkashin wannan yarjejeniya, amma Amurka ta fice daga yarjejeniyar domin neman cimma bukatarta ta ci gaba da kawo rudani da takaddama kan Shirin kasar ta Iran na makamashin nukiliya na zaman lafiya..

A gefe guda kuma, shugaba Pezeshkian ya tabo mawuyacin halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma abubuwan da suka faru a Zirin Gaza da Lebanon, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da kuma  laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Gaza da Lebanon musamman aiwatar da laifin kisan gilla ga shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh, don cin fuska a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan zubar da jinin ‘ya’yayensa da jikokinsa a Gaza da kuma ayyukan ta’addanci kan al’ummar Falasdinu, lamarin da ya wurga yankin cikin mummunan rikici.

Pezeskian ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya sun keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa da suka hada da kashe mata da yara da kai hare-hare kan cibiyoyin kula da kiwon lafiya da asibitoci da jefa bama-bamai kan makarantu da matsugunan ‘yan gudun hijira, sai dai a maimakon tsawatar da ita daga kasashen da suke da’awar kare hakkin bil’adama, abin takaici sune ke ba ta goyon baya da kuma karfafa ta da makamai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments