Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Imanin Iran Da Tattaunawan Zaman Lafiya Amma Ba Za Ta Amince Da Barazana Ba

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba

A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana.

Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari É—aya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima. Iran ta yi imani da tattaunawa da zaman lafiya, amma ba za ta taba mika wuya ga barazana da umarni ba.

Sugaban kasar ya kara da cewa: Ci gaba da kuma cimma manyan buruka na bukatar azama, karfin gwiwa, da kuma sauya yanayin tafiyar da harkokin gudanarwa. Idan wani ya yi niyya don ya cimma manufa amma ya yi kasa a gwiwa a farkon mataki, to ba zai taba cimma burinsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted