Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Suke Da Hakkin Yanke Shawarar Makomar Kaarsu Ba Amurka Ba

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin da Trump ya kakabawa kasarsa.

A jawabin da shugaba Pezeshkian ya gabatar a wajen taron shugabannin lardin Tehran ta yamma da majalisar gudanarwa ta garuruwan Mallard, Shahriar da Quds, shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa, ma’anar gudanarwa ita ce sanin damammaki da barazana a ciki da wajen kasar da kuma sanin irin karfi da ake da shi.

Shugaban kasar ya jaddada cewa: Trump na fadin wani abu, kuma wasu mutane sun saba da abin da Trump yake so. Mene ne Trump yake son aikatawa? A nan mu ne za mu yanke shawarar yadda za mu tafiyar da makomarmu. Idan ba Iran ba ta canza ra’ayinta ba, to, ta sanya wa kanta takunkumi a hukumance, amma idan ta sauya ra’ayinta, Trump ba zai kai ma burinsa ba, kuma komai yawan takunkumin da zai Sanya kan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments