Pezeshkian: Ana Ci Gaba Da Keta Hakkin Dan Adam A Gaza

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ana ci gaba da keta hakkin bil’Adama a Gaza amma kasashen da suke babatun kare hakkin dan Adam sun

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ana ci gaba da keta hakkin bil’Adama a Gaza amma kasashen da suke babatun kare hakkin dan Adam sun yi shiru 

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayin da ya karbi bakwancin fira ministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani a jiya Litinin ya yi nuni da cewa, a duk sa’o’i da mintuna ana keta hakkin bil’adama da kuma dukkanin dokokin kasa da kasa a Gaza, amma babu wani mataki da kasashen da suke da’awar kare hakkin dan Adam suke dauka ko cewa uffan kan lamarin.

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Babban abu mafi muni, ba wai kawai sun yi shiru a kan waɗannan laifuka ba ne, amma suna goyon bayan masu aikata waɗannan laifuka da kisan kare dangi kan wata al’umma.

Shugaba Pezeskian ya ci gaba da cewa: Kasashen musulmi da sauran kasashen da suke da ra’ayin kiyaye tsare-tsare da dokoki na kasa da kasa sun tsaya tsayin daka, tare da daukar matakai na hadin gwiwa, domin tilasta wa magoya bayan yahudawan sahayoniyya don kawo karshen wannan bakar siyasa ta zalunci da kuma dakatar da laifuka da kisan kare dangi a Gaza.

A nasa bangaren, fira ministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa: Sarkin Qatar yana ba da muhimmanci ta musamman wajen fadada huldar ‘yan uwantaka da manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, kuma ya jaddada cewa dole ne mu kara himma wajen cimma wannan buri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments