Kafofin yada labaran kasar Iraki sun yi nuni da cewa: Ziyarar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya kai zuwa kasar Iraki tana nuni da muradin sabuwar gwamnatin Iran na karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma bunkasa fahimtar juna da aka kulla tsakanin Iran da Iraki, baya ga rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu a fannin tsaro da tattalin arziki.
Kafofin yada labarai sun yi nuni da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Iran da Iraki, yayin da yawan musayar cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 10 a duk shekara, kuma kasashen biyu na fatan kara wannan matsayi zuwa dala biliyan 20.
Wadannan majiyoyin sun yi hasashen cewa, batutuwan yanki da na kasa da kasa za su kasance a kan teburin tattaunawa da shugaba Pezeshkian zai yi da shugaba Abdul Latif Rashid da fira minista Muhammad Shiya Al-Sudani, musamman dangane da ci gaba da cin zarafin ‘yan ta’addar sahayoniyya a Zirin Gaza da kokarin da ake yi na tsagaita bude wuta.