Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen musulmi tana rusa makircin makiya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran mamba ce mai muhimmaci a cikin rukunin kasashe 8 na hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen musulmi (D8), yana mai bayanin cewa idan suka ci gaba da kyautata alaka tsakaninsu na musulmi, to za su iya rusa makircin makiya da suke tunkarar musulmi.
Kafin ya tashi daga birnin Tehran zuwa birnin Alkahira domin halartar taron kolin D8, shugaba Pezeshkian ya kara da cewa: Taruka a wannan matakin na da matukar amfani da tasiri ga harkokin diflomasiyya mai muhimmaci ta yadda kasashen musulmi za su kara samun kusanci da juna a fannonin tattalin arziki, siyasa, al’adu da zamantakewa da kuma musayar harkokin ci gaba a tsakaninsu.
Pezeshkian ya bayyana kasar Masar, a matsayar kasar da ta karbi bakwancin zaman taron, a matsayin wata tsohuwar kasa mai matukar wayewa, inda ya ce Masar kasa ce da ke da tasiri a duniyar musulmi, ya kara da cewa: ya gana da shugaban kasar Masar, tare da gudanar da kyakkyawar tattaunawa da shi a gefen zaman taron kasashen kungiyar BRICS da aka gudanar a watan jiya a birnin Qazan na kasar Rasha.