Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya
Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba.
Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi.
Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta hadin gwiwa, shugabannin kasashen musulmi za su iya ba da misali mai kyau na zaman tare da samun bunkasar wadata.
Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Iran a shirye take ta fadada alakar ta da Saudiyya ta kowane fanni.