Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a wanda aka gudanar a nan Tehran.
Shugaban ya kara da cewa, Iran bata neman yaki da kowa, amma zata maida martani kan duk wata takala daga HKI ko Amurka. Ya ce Iran ba zata amince wani ya hana mutanen kasar amfani da fasahar da All..ya hore masu ba. Ya kuma kara jaddada cewa JMI bata neman mallakar makaman Nukliya.
A rana irin ta yau ce wato 9 ga watan Afrilun shekara ta 2006, masana fasahar nukliya na JMI suka sami nasara a karon farko suka samar da makamashi daga fasahar nukliya tare da amfani da sinadarin Uranium.
A yau shekaru 19 kenan tun lokacin kasar take samun ci gaba a fasahar Nukliya da kuma amfaninsa. Inda ya ma kasar ta kaddamarda sabbin ci gaban da ta samu tare da amfani da makamacin Nukliya.