Shugaban Kasar Iran Ya Bukaci Hadin Kan Musulmi Don Fuskantar HKI Da Kasashen Yamma

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bukaci hadin kan musulmi a duniya don fuskantar HKI da kuma kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bukaci hadin kan musulmi a duniya don fuskantar HKI da kuma kasashen yamma.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar, ya kuma kara da cewa, da musulmi a duniya zasu hada kai HKI da kasashen yamma ba su isa su aikata kissan kare dangin da suke yiwa Falasdinawa a Gaza ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a hubbaren Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JMI da ke kudancin bernin Tehran, saboda, da shi da majalisar ministocinsa da kuma sauran Jami’an gwamnatinsa su jajjada bai’a ga ikidu da kuma ra’ayoyin wanda ya kafa JMI.

Har’ila yau, a yau ne aka fara makon gwamnati a nan kasar Iran, don tunawa da shahadar tsohon shugaban kasar Dr Ali Raja’i da firai ministana a lokacin sanadiyar tashin bom a ofishins firai minister na lokacin.

HKI dai ta fara yaki a Gaza ne, tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, kuma ya zuwa yanzu an kashe Falasdinawa fiye da dubu 40, mafi yawansu mata da yara, sannan wasu fiye da dubu 93 sun ji rauni.

Dangane da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar Iran kuma, Pezeskiyan ya bayyana cewa kamar yadda yan kasar Iran suka hada kai a farkon juyin juyha halin musulunci a kasar, suka sami nasara a kan kasashen duniya gaba daya wadanda suka dorawa kasar yaki, a halin yanzu ma, tare da hadin kan mutanen kasar babu wata matsala wacce ba za’a maganceta ba.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments