Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Yana fatan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshgan ya bayyana cewa: Iran tana fatan tattaunawarta da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.
A yammacin jiya Lahadi, a gefen taron dandalin tattaunawa na Tehran na shekara ta 2025, a wata ganawa da ministan harkokin wajen masarautar Oman Badar bin Abdullah al-Busaidi, Shugaba Pezeshkian ya yaba da irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma irin rawar da gwamnatin Oman take takawa wajen daukar nauyin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Yana mai cewa: “Suna fatan sakamakon kokari da kuma sahihan manufofin Sultan Haitham bin Tariq, wadannan shawarwarin za su kai ga cimma yarjejeniyar adalci da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”
Shugaban na Iran ya jaddada wajabcin kara samun kusanci a tsakanin kasashen musulmi, yana mai cewa “masu kusanci da juna da fadada hadin gwiwarsu, haka nan masu fatan cutar da al’ummar musulmi za su zama masu haifar da sabani da rabuwar kai a tsakaninsu.”