Shugaban Kasar Iran: Tsarin Kiwon Lafiya A Iran Abin Koyi Ne Ga Kasashen Yanki Da Duniya

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan  wanda ya girmama ma’aikatan kiwon lafiya a birnin Mashahd ya bayyana cewa; Tsarin kiwon lafiya da ake da shi a

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan  wanda ya girmama ma’aikatan kiwon lafiya a birnin Mashahd ya bayyana cewa; Tsarin kiwon lafiya da ake da shi a Iran,musamman a fagen kiwon lafiya na tushe ya zama abin koyi da samun irinsa ya karanta a cikin wannan yankin na yammacin Asiya da kuma a duniya baki daya.

Shugaba Fizishkiyan ya kuma yi ishara da fagagen kiwon lafiya da Iran ta yi fice a cikinsu da su ka hadada  kula da mata masu juna biyu, dakile cutukan da ake  iya dauka, da kuma wayar da kan mutane akan batutuwa masu alaka da kiwon lafiya, sai kuma koyar da ilimin likitanci ga masu tasowa.

Shugaban kasar ta Iran ya yi ishara da kididdigar da take nuni da cewa ana kara samun tsawon rayuwa a Iran, haka nan kuma raguwar mutuwar kananan yara.

Haka nan kuma shugaban kasar na Iran ya yi ishara da inshora ta kiwon lafiya da likitoci na iyalai da ake da su, tare da yin ishara da rawar da suke takawa a fagen kiwon lafiya a cikin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments