Shugaban Kasar Amurka Ya Zanta Ta Wayar tarho Da Benyamin Natanyahu Dangane Da Iran Da Gaza

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zanta ta wayar tarho da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu kan kasar Iran da kuma yakin Gaza. Kamfanin dillancin

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zanta ta wayar tarho da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu kan kasar Iran da kuma yakin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majiyar ofishin Natanyahu ta bayyana cewa tattaunawar tana zuwa ne a dai-dai lokacinda rikici da yaki yake ci gaba a gaza, da kuma tattaunawa kan shirin Nuclear kasar Iran ke ci gaba.

Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Amurka na jirin jawabin da kasar Iran zata mayar masa dangane da shawarar da ya gabatar na warware matsalar tashe makamancin Yuranium a Iran.

Har’ila yau ya na jiran jawabin da kungiyar Hamas za ta bayar kan yarjeniyar  dakatar da yaki a Gaza.

Shugaban dai yana cikin matsin lamba don ganin an warware wadannan al-amura guda biyu na gabas ta tsakiya.

Tattaunawar wanda bai fi mintoci 40 ba, ya bukaci gwamnatin Natanyaho ta shirya daukar matakan gaggawa bayan da shugaban ya sami wadannan sakonnin da yake jira.

Don haka ne ake saran Natanyanhu zai gudanar da taron gaggawa tare da manya manyan jami’an gwamnatinsa a ma’aikatar tsaro ko yakin na kasar, don tattauna wadannan al-amura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments