Shugaban Kasar Amurka Ya Sake Jaddada Matsayinsa Dangane Da Gaza A Ganawarsa Da Sarkin Jordan

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba.

A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad  bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke da shawarorin da zasu gabatar dangane da wannan matsalar.

Sarkin ya kara da cewa a halin yanzu dai kasarsa za ta dauki yara kanana kimani 2000 marasa lafiya, wadanda suke fama da cutar kansa a Gaza don jinyarsu a kasar Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments