Shugaban Kasar Amurka Ya Kara Yawan Kasashen Da Ya Sa Wa Takunkumin Shiga Amurka

Shugaban kasar ta Amurka Donald Ttump ya kara yawan kasashen da ya sa wa takunkumin shiga cikin Amurka zuwa kasashe 43. Daga cikin kasashen da

Shugaban kasar ta Amurka Donald Ttump ya kara yawan kasashen da ya sa wa takunkumin shiga cikin Amurka zuwa kasashe 43.

Daga cikin kasashen da ya sa wa sharuddan shiga cikin kasar Amurka sun hada guda 11 da su ne; Somaliya, Sudan, da Libya. Sai kuma Afghanistan, Cuba, Iran, Korea Ta Arewa, Syria, Venezuela da kuma Yemen.

A lokacin zangonsa na farko Trump matakin nasa ya ja hankalin duniya saboda yadda ya hana ‘yan hijira daga kasashen Iraki,  Libya, Somaliya, Sudan da Yemen shiga cikin kasar.

An kalubalanci matakin na shugaban kasar Amurka a wancan lokacin a kotu saboda yadda ya shafi mafi yawancin kasashen musulmi.

Bayan da Joe Biden ya zama shugaban kasa ya soke wancan matakin na Donald Trump a 2021.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments