Shugaban Iran Ya Yi Gargadi Game Da Makircin Kasashen Waje Na Wargaza Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Iran ya yi gargaɗi game da makircin ƙasashen waje na wargaza ƙasashe Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da membobin majalisar ministocinsa sun sabunta alƙawarin

Shugaban Iran ya yi gargaɗi game da makircin ƙasashen waje na wargaza ƙasashe

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da membobin majalisar ministocinsa sun sabunta alƙawarin da suka ɗauka na bin ƙa’idodin wanda ya kafa juyin juya halin Musulunci, Imam Khomeini (Allah ya yi masa rahama), a hubbarensa mai tsarki da ke birnin Tehran, wanda ya yi daidai da fara bukukuwan “Kwanaki Goma na Alfijir”, na cikan shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran.

Shugaba Pezeshkian ya ajiye fure a hubbaraen mu’assasin juyin juya halin, Ayatollah Imam Khomeini (Allah ya yi masa rahama), sannan ya karanta Fatiha ga ruhinsa, yana mai sabunta alƙawarin da suka yi wa ƙa’idodin marigayi Imam da shahidai.

A jawabinsa bayan bikin jaddada rantsuwar, Shugaba Pezeshkian ya yi gargaɗi game da ƙoƙarin maƙiya na amfani da zanga-zangar jama’a da kuma ingiza su zuwa ga kunna wutar rikici a cikin gida wanda ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar. Ya jaddada cewa abubuwan da suka faru kwanan nan sun nuna yunƙurin da aka shirya don tayar da tarzoma da kuma zagon kasa ga tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted