Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya Na Kudancin Yemen Ya Isa UAE Bayan Ya Arcewa Daga Yankin

Shugaban gwamnatin Rikon kwarya na kudancin kasar Yemen mai samun goyon bayan kasar UAE Aidrous al-Zubaidi ya isa birnin Abudhabi daga yankin SomaliLand Tashar talabijan

Shugaban gwamnatin Rikon kwarya na kudancin kasar Yemen mai samun goyon bayan kasar UAE Aidrous al-Zubaidi ya isa birnin Abudhabi daga yankin SomaliLand

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa Aidrous al-Zubaidi wanda yake samun goyon bayan gwamnatin Hadaddiyar daulolin larabawa wanda kuma yake son shelenta ballewar kudancin kasar Yemen daga arewacin kasar ya arce daga birnin Aden babban birnin yankin zuwa lardin Somaliland kafin ya wuce zuwa birnin Abudhabi.

A wani bayanin da jam’iyun hadaka a kudancin kasar ta Yemen suka bayyana a safiyar yau Alhamis, sun ce Zubaidi ya sulale cikin dare inda ya haw kole-kule wanda ya tsara da shi tekun Aden ya kuma sauke shi garin bakin ruwa na Berberan a yankin Somalilan, sannan daga baya tare da taimakon kwamandan sojojin UAE a Somaliland Janar Awad Saeed ya taimaka masa ya isa birnin Abudabi.

Wasu labaran sun bayyana cewa gwamnatin UAE ta dauko masa jirgi na musaman Ilyushin I1-76 wanda ya dauke shi da wadanda suke tare da zuwa zuwa Magadishi da farko sannan ya karasa zuwa birnin Abudabi daga can.

Kasar Hadaddiyar daular Larabawa da Saudiya suna rikici a cikin yan kwanakin da suka gaba kan yadda al-amura suke tafiya a kudancin kasar ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted