Salmiya: Sojojin Isra’ila Sun Azabtar Da Ni

Daraktan asibitin al-Shifa na Gaza, wanda sojojin Isra’ila suka  tsare da shi sama da watanni bakwai, ya ce an gallaza masa azaba mai tsanani a

Daraktan asibitin al-Shifa na Gaza, wanda sojojin Isra’ila suka  tsare da shi sama da watanni bakwai, ya ce an gallaza masa azaba mai tsanani a lokacin da ake tsare da shi a gidajen yarin Isra’ila.

Mohammed Abu Salmiya na daga cikin Falasdinawa sama da 50 da Isra’ila ta sako da suka koma Gaza, a cewar wata cibiyar  lafiya a yankin.

Salmiya ya shaida wa taron manema labarai a ranar Litinin cewa fursunonin suna fuskantar kowane nau’i na azabtarwa a cikin gidajen yari da wuraren da ake tsare da su a hannun Isra’ila.

“Kusan ana azabtar da su kullum. An shiga dakuna – dakuna ana kuma dukan fursunoni.”

“ Fursunonin da dama sun mutu a cibiyoyin bincike kuma ana hana su abinci da magunguna,” in ji shugaban asibitin.

Salmiya ya ce masu gadin gidan yarin na gwamnatin yahudawa sun karya dan yatsansa na hannu, sannan kuma suka yi masa rauni a kansa wanda ya yi ta zubar da jinni yayin da ake dukansa, inda suka yi amfani da sanduna da karnuka wajen azabtar da shi.

A cewarsa, wuraren da ake ajiye Falastinawa da Isra’ila take tsare da su, ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa ta fuskar kiwon lafiyar dan adam.

Wasu Falasdinawa da ake tsare da su, in ji shi, an yanke sassan jikinsu saboda rashin kula da lafiya.

Salmiya ya kara da cewa, har yanzu akwai dubban fursunonin da ke hannun sojojin gwamnatin yahudawan Sahyuniya.

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, yanayin sabbin fursunonin da aka sako yana nuna alamun bacin rai da azabtarwa ta jiki da ta hankali, wanda kuma hakan ya fallasa irin laifuffukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments