Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su
Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar.
Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai tafka babban kuskure a manufofin siyasar na harkokin waje tun farko fara gudanar da mulkinsa karo na biyu, a lokacin da ya firgita manema labarai inda ya shaida musu cewa yana so ya share ‘yan Gaza daga mazaunansu tare da kwashe wasu daga cikinsu zuwa kasashen Jordan da Masar.
Akwai yiwuwar shawarar Trump ta zo ne a matsayin ra’ayinsa na kashin kansa, ba hakikanin siyasar da zai aiwatar a zahiri ba, sai dai fitar kalaman a fili ta bai wa shugabannin Larabawa masu sassaucin ra’ayi da suke neman yin aiki da shi ta wurga su cikin mamaki, domin canjawa Falasdinawa wurin zama lamari ne da zai dagulawa gwamnatocin kasashen Larabawa masu sassaucin ra’ayi lissafi a duk yankin.
Ignatius ya kara da cewa: Trump a matsayinsa mai son kawo rudani zai iya furta kalaman a matsayin ra’ayinsa na tabbas a fagen siyasarsa a yankin Gabas ta Tsakiya, wadda ta kasance kamar jefa bama-bamai kan kasashen Larabawa.