Shugaban kasar Amurka Trump ya ce: Za su dauki matakin soji kan kasar Venezuela nan ba da jimawa ba
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da cewa kasarsa za ta iya fara yaki da “masu safarar miyagun kwayoyi nan ba da jimawa ba,” yana mai cewa, “Za su dauki mataki ta hanyar kutsawa ta kasa a kasar Venezuela,” yana mai nuni da yiwuwar shiga tsakani na soja ko ayyukan leken asiri.
A martanin da ya mayar, Shugaba Trump daga baya ya musanta rahotannin cewa: Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da kan iyakar Venezuela, yana mai jaddada cewa: “Ba gaskiya ba ne cewa: Amurka ta aika da jiragen yakin sama kusa da Venezuela.”
Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House cewa: “Rahotanni daga kafofin watsa labarai game da aika jiragen yakin sama na B-1 zuwa kan iyakar Venezuela ba su dace da gaskiya ba.”
Trump ya kara da cewa: Gwamnatinsa ba za ta nemi Majalisar Dokoki ta “yi shelar yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ba; za su kashe su kawai.”