Shugaban Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila Netanyahu ba zai ja shi zuwa shiga cikin yaki da Iran ba, kuma a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada cewa: Ba za a sanya shi shiga yaki da Iran ba saboda manufofin fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Trump ya kara da cewa a wata hira da ya yi da mujallar Time, a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci ko kuma shugaban kasar Iran.
Duk da imanin da ya yi cewa: Amurka da Iran za su iya cimma yarjejeniya, amma Trump ya sake nanata barazanarsa na cewa idan ba a cimma matsaya ba, to zai bi sahun ‘yan yahayoniyya wajen kai wa Iran hari, domin ganin cewa, Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.
Trump ya kuma musanta yunkurin cewa zai hana Isra’ila kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran.