Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Ya Jaddada Aniyarsa Ta Korar Bakin Haure Daga Amurka

Zababban shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Za su fara gudanar da aikin korar baki mafi girma a tarihin Amurka Zababban shugaban kasar Amurka mai

Zababban shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Za su fara gudanar da aikin korar baki mafi girma a tarihin Amurka

Zababban shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi alkawarin fara gudanar da aikin korar bakin haure mafi girma a tarihin Amurka da zarar sabuwar gwamnatinsa ta fara aiki.

Trump ya kara da cewa: Zai gudanar da manyan sauye-sauye a Amurka kuma ‘yan jam’iyyar Republican masu rinjaye a majalisar dokokin kasar suna goyon bayan nade naden sabbin jami’ai da ya sanar.

Trump ya bayyana cewa: Amurka zata daina shiga yaki a kasashen waje wadanda ba su da amfani na banza. Sannan yana jiran ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin domin warware rikicin kasar Ukraine

Haka nan Trump ya yi da’awar cewa: Abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Oktoba a haramtacciyar kasar Isra’ila da yaƙin Ukraine da ba su faru ba idan ya kasance shugaban Amurka a lokutan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments