Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu.
Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka tabakin mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai Bayo Onanuga a jiya Alhamis.
Shugaban ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan murmurewar wadanda suka ji rauni. Ya kuma bukaci a gaggauta gudanar da bincike don sanin abinda ya haddasa hatsarin day a kai da wannan asarar, don daukar matakan hana aukuwar irinsa nan gaba.