Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin.
Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon.
Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken da za a daga a yayin jana’izar shi ne; “Muna Nan A Kan Riko Da Alkawali.”
A gefe daya, Sheikh Na’im Kassim ya yi Magana akan yadda sojojin HKI suke ci gaba da keta tsagaita wutar yaki, tare da yin kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da su ka dace.
Haka nan kuma babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya jinjinawa jaruntar mutanen kudancin Lebanon da su ka kutsa cikin garuruwansu duk da cewa, sojojin HKI suna ciki, domin isa gidajensu.