Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen. Wadanda sojojin HKI suka kashe ko suka kaisu ga shahada a shekarar da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da kuma al-amura da suke faruwa a duniya gaba daya.
A cikin jawabin da ya gabatar a taron jana’izar dai, sheikh Qasim ya bayyana cewa kungiyar Hizbullah zata ci gaba a kan tafarkin Shahid Hassan Nasaralla. Sannan al-amura da dama sun sauya, don haka zasu yi aikin bisa abinda suka ga ya dace a ko wani lokaci.