Senegal ta yi Allah-wadai da tsare ‘yan kasarta a Mauritania

Ministar Harkokin Wajen Senegal, Yacine Fall, ta ce hukumomin kasarta sun bayyana rashin jin dadi game da tsare ‘yan Senegal da kuma tilasta musu barin

Ministar Harkokin Wajen Senegal, Yacine Fall, ta ce hukumomin kasarta sun bayyana rashin jin dadi game da tsare ‘yan Senegal da kuma tilasta musu barin kasar bisa zarginsu da zama cikin Mauritania ba bisa ka’ida ba.

Hukumomin kasar Mauritaniya sun kaddamar da wani gangamin korar bakin haure daga kasashen Afirka daban-daban.

A wani jawabi da ta gabatar yayin taron amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar ta Senegal kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa Fall ya ruwaito,  “kowace kasa tana da nata dokoki, amma rashin samun takardar zama ko takardar izinin aiki a cikin sa ba zai taba hujja ta cin zarafi ba.

Majalisar dokokin kasar Senegal ta yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta daukar matakai don ganin an warware matsalar a’yan kasar da suke zaune a Mauritania,” tana mai bayyana abin da Mauritania ke yi a matsayin “cin zarafin bil’adama.”

A nata bangaren, ma’aikatar harkokin wajen kasar Mauritaniya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce kasar ta tabbatar da bude kofa ga bakin haure tare da karfafa tare da yin komai a cikin  tsari, da kuma shiga kasar cikin kasar bisa sharudda da suke a a kan doka, tana mai cewa “Mauritaniya tana maraba da baki da ke zama a cikin kasarta bisa doka kuma cikin yanayi mai kyau, musamman wadanda suka fito daga kasashe makwabta.”

Ta kuma yi nuni da cewa, yin kaura ba bisa ka’ida ba a wasu lokuta ya kan zama barazana ga yanayin zaman lafiya da tsaron kasa, a kan haka ne take kokarin tantance yanayin baki mazauna kasar, amma hakan ba zai yi tasiri a kan alakar da ke tsakaninta dad a kasashen dab akin suka fito ba, kuma za a warware batun  ta hanyar fahimtar juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments