Sayyid Fadhlullahi Ya Jaddada Muhimmanci Samar Da Makamai Ciki Har Da Kare Kasa Daga Dan Mamaya

Sayyid Fadlallah ya bayyana cewa: Ana samar da makamai ne domin kare kasa da kuma matsa wa abokan gaba A cikin hudubar sallar Juma’arsa daga

Sayyid Fadlallah ya bayyana cewa: Ana samar da makamai ne domin kare kasa da kuma matsa wa abokan gaba

A cikin hudubar sallar Juma’arsa daga mumbarin masallacin Imamain al-Hassanain (amincin Allah ya tabbata a gare su) da ke Haret Hareik a kudancin birnin Beirut, Sayyid Ali Fadlallah ya yi kira da a dauki dukkan matakai na tursasawa makiya yahudawan sahayoniyya janyewa daga yankin kasar Lebanon da ta mamaye, da daina kai hare-haren wuce gona da iri kullum rana kan yankunan Lebanon, da kuma sakin mutanen da suka kama a matsayin fursunonin yaki.

Malamin ya bukaci dukkanin ‘yan kasar Lebanon, ba tare da la’akari da mazhabobin su ba, ko kungiyoyinsu, ko kuma matsayinsu na siyasa, da su tashi tsaye wajen gudanar da hakkokin da sukarataya a wuyarsu kan kasarsu, da kuma fuskantar wadanda ke yin zagon kasa ga ikon kasa da tsaro, da zaman lafiyarta, da kuma samun hadin kan muryarsu wajen tunkarar wadannan hare-haren da ke barazana ga zaman lafiyar cikin gida da zaman dukkan al’umma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments