Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Abin da ke faruwa a Falasdinu wani muhimmin gwaji ne ga al’ummar yankin
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul-Malik Badarudden al-Houthi, ya jaddada cewa: Musulmi a Gaza suna fama da munanan hare-haren wuce gona da iri da kisan kiyashi da suke tada hankalin bil’adama a kasashen da ba na musulmi ba.
A jawabin da ya yi kai tsaye ga al’ummar Yemen, Sayyid Al-Houthi ya yi nuni da cewa: Wasu gwamnatocin sun fito fili suna hada kai da taimakekkeniya da makiya yahudawan sahayoniyya da kuma biyayya gare su, lamarin da ya kasance abin babban abin kunya.
Sayyid Al-Houthi ya jaddada cewa: Shugabannin kafirci da sharri da zalunci da wuce gona da iri sun zama masu mulki kan al’umma, don haka suke kokarin wurga al’ummunsu cikin ramin halaka ta hanyar yada fasadi da bata.