Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan a wata ganawa da ya yi da Ali Bagheri, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Haniyeh da kuma matakin wuce gona da iri kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi, ya bayyana halin da ake ciki a yankin da cewa. mai cike da hadari”.
Ministan riko na harkokin wajen kasar Iran, Ali Bagheri ya tattauna ta wayar tarho a jiya Alhamis da ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Amir Faisal Bin Farhan kan sabbin al’amura da suka shafi shahadar Ismail Haniyeh shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da gwamnatin sahyoniya ta yi.
Shugaban hukumar kula da harkokin diflomasiyya ta Iran ya ce Gwamnatin sahyoniya ta ketare jan layi ta hanyar aikata wannan ta’addi.
Ya kuma jaddada cewa: Iran za ta yi amfani da hakki da halaccinta wajen daukar mataki kan gwamnatin sahyoniyawan ta za ta fuskanci nadama har abada.
Balqheri ya kara da cewa: Taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya zama wajibi domin tinkarar manyan laifukan gwamnatin sahyoniyawan da ta yi na kisan Isma’il Haniyyah da kuma keta hurimin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.