Saudiyya Ta Jaddada Rashin Amincewa Da Tilastawa Falasdinawan Zirin Gaza Yin Gudun Hijira

Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah

Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza

Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu.

Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na tsattsauran ra’ayi na ‘yan mamaya baya daukan Falasdinu a matsayin kasar Falastinu wacce take matsayar kasar gado da tarihi da shari’a suka tabbatar da hakan, kuma ‘yan mamaya ba su la’akari da cewa tun farko al’ummar Falastinu sun cancanci rayuwa; Don haka suka rusa yankin Zirin Gaza gaba daya, tare da kashe mutane fiye da dubu 160, wadanda akasarinsu yara da mata ne, ba tare da kiyaye dokokin kasa da kasa da na hakkin dan Adam ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments