Saudiyya : Alhazai 1,301 Ne Suka Rasu A Yayin Aikin Hajjin Bana

Hukumomi a Saudiyya sun ce alhazai 1,301 ne suka rasu lokacin aikin Hajjin, kuma yawancin wadanda suka rasun wadanda basuyi rajista ba ne. Abin takaici

Hukumomi a Saudiyya sun ce alhazai 1,301 ne suka rasu lokacin aikin Hajjin, kuma yawancin wadanda suka rasun wadanda basuyi rajista ba ne.

Abin takaici shi ne, mutanen da suka mutu sun kai 1,301, kuma kashi 83 daga cikinsu sun zo aikin Hajji ne ba tare da izini ba inda suka yi tafiyar-kafa mai tsawo cikin tsananin zafin rana, ba tare da makwanci ko kulawa ba,” in ji wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Saudiyya Saudi Press Agency ya bayar ranar Lahadi.

Kafin nan dama wasu jami’an diflomasiyya na kasashen Larabawa sun shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP a makon jiya cewa ‘yan kasar Masar 658 ne suka rasu, kuma 630 daga cikinsu ba su yi rajistar aikin Hajji ba.

Jami’an na diflomasiyya sun ce yawancin mutanen sun rasu ne sakamakon tsananin zafi.

Ministan Ma’aikatar Lafiya na Saudiyya, Fahd al Jalajel, ranar Lahadi, ya bayyana Hajjin bana a matsayin wanda ya yi “nasara”, kamar yadda SPA ya ruwaito.

Ya ce ma’aikatar lafiya ta “kula da lafiyar fiye da mutum dubu 465 cikinsu har da mutum dubu 141 da ba su da takardar izinin aikin Hajji.”

Hukumomin Saudiyya sun ce mutum fiye da miliyan 1.8 suka gudanar da Hajjin bana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments