Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza

Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da

Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion.

Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza.

Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu  linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman ne daga kasar Yemen.

An ji karar fashewar wasu makamai masu linzami a sassan tsakiya na Falastinu da Isra’ila ta mamaye da hakan ya hada da kewayen birnin al-Quds. Kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a babban filin jirgin saman Ben Gurion sakamakon wadannan hare-hare na dakarun Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments