Salami: Babu Inda Ba Za Mu Iya Kai Wa Hari Ba A Fadin HKI

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru.

Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa;  Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama.

A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Ministan tsaron na Iran Laftanar janar Azizi Nasri Zadeh ya kara da cewa;  Idan har yaki ya barke, to za a tilasta wa Amruka ficewa daga wannan yankin, kuma asarar da za ta yi sai ta rubanya wacce za ta yi wa Iran.”

Ministan tsaron na Iran ya kuma ce; Abin takaici ne yadda wasu jami’an Amurka su ka yi barazanar yiyuwar barkewar yaki, idan ba a cimma matsaya ba a tattaunawar Nukiliya, sannan ya kara da cewa: Tehran ba ta maraba da yaki, amma kuma a lokaci daya ta shirya masa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments