Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba.
A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba.
Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi la’akari da kalubalen da ake fuskanta, gwamnatin rikon kwaryar Siriya “watakila a ‘yan makwanni, ba watanni ba, da yiwuwar durkushewarta da kuma bullar yakin basasa, wanda gaba daya zai haifar da wargajewar kasar.”