Rundunar Sojojin Iran ta yi tir da matakin EU kan dakarun IRGC

Rundinar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da wata sanarwa tana mai mayar da martani ga matakin da kungiyar Tarayyar Turai ta dauka na

Rundinar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da wata sanarwa tana mai mayar da martani ga matakin da kungiyar Tarayyar Turai ta dauka na ayyana Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “ƙungiyar ta’addanci,”

Rundinar tana mai Allah wadai da matakin da ta danganta a matsayin haramtacce, wauta, da kuma manufar siyasa.

A cikin wannan sanarwa, Babban Hafsan sojojin na Iran ya bayyana matakin a matsayin nuna kiyayya ga al’ummar Iran, sojojinsu, da tsaron kasa da ‘yancin kai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Babban Hafsan ya jaddada cewa an yanke wannan shawara ne a karkashin matsin lamba kai tsaye daga shugaban Amurka da gwamnatin Isra’ila.

Sanarwar ta tunatar da cewa Dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) wata hukuma ce halatacciya, mai karfi wadda ta kasance a sahun gaba wajen yaki da ta’addanci, da Amurka da gwamnatin Isra’ila ke goyon baya.

Janar din ya kuma nuna sadaukarwar da IRGC ta yi a yaki da kungiyoyin ta’addanci irinsu ISIS.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted