Rundunar sojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa: Sojojin yahudawan sahayoniyya 668 suka halaka tun bayan kaddamar da yaki kan Zirin Gaza naFalasdinu
Alkaluman da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fitar na nuni da cewa: Adadin sojojin yahudawan sahayoniyya da aka kashe tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, sun kai 668, ciki har da 314 da suka sheka lahira a yayin yakin kasa da suke yi a Zirin Gaza.
A tsawon kwanaki 269 da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kwashe suna ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen Turai, inda jiragensu suke yi ruwan bama-bamai a kan asibitoci, gine-gine, hasumiyoyi, da gidajen fararen hula na Falasdinawa tare da ruguza su a kan kawunan Falasdinawa da suke rayuwa a cikinsu gami da hana shigar da kayan abinci, ruwa, magunguna da makamashi musamman man fetur cikin yankin.
Rahotonnin kasa da kasa sun bayyana cewa: Ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin kan Gaza ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa 37,900 tare da jikkata wasu 87,600 na daban, baya ga raba Falasdinawa kimanin miliyan 1 da dubu 700 da muhalillinsu, a cewar bayanan Majalisar Dinkin Duniya.