rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump.
Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi.
A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji shi, sannan ya kara kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi gaggawar daukar matakin magance matsalar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, inda shugaban kasar Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa cewa babu wata barazana da kiristocin kasar suke fuskanta.