Farfagandar Trump

1 “Babu abin da ya faru da mu!”, Dubi zuwa ga da’awar tawagar Trump. 2 Bari mu sake yin dubi tare ku kan hakan. An

Share

Hoton Trump da yanayin yaki

1

“Babu abin da ya faru da mu!”, Dubi zuwa ga da’awar tawagar Trump.

2

Bari mu sake yin dubi tare ku kan hakan. An rusa tsarin tsaro na Iran baki daya, an wargaza rundunar sojojinta na ruwaa, an kawar da shugabanninta da kwamandojinta gaba daya, kuma an lalata kayayyakinta na more rayuwa.

3

Wannan shi ne abin da Trump da tawagarsa da kafofin watsa labaransu suka fada tun daga farkon yaki kuma suke ta maimaitawa.

4

Amma tambaya mai sauki da ta yi karo da wannan da’awa ita ce:
Idan dai har an kawo karshen komai a kasar, to me yasa jiragen saman yaki suke bacewa a sararin samaniyar kasar?

5

Duk da haka, labarin da wasu kafofin yada labarai suke bayar ya yi hannun riga da wannan tunanin. Inda suke cewa kasar ba wai kawai ba ta ruguje ba, har ma tana ci gaba da tabbatar da ikonta a kan mashigar Hormuz, hanyar ruwa mai muhimmanci wajen fitar da makamashi a duniya.

6

Sannan kuma suna tambaya kan cewa, idan har babu abin ya rage a kasar, me yasa har yanzu dakarun kasar suke kai hari da lalata kadarori a sansanonin Amurka da ke cikin kasashen yankin Tekun farisa? A cewarsu wannan yana nuna babban gibi tsakanin labarai na gwamnati da kuma gaskiyar abin da yake faruwa a kasa!

7

Mafi yawan kafofin yada labarai na gwamnati a Amurka suna nuna samun nasara a koda yaushe a kan abokna gaba. Haka kuma Trump da tawagarsa suna tinkaho da karfinsu, tare da yin izgili ga wanda ya saba ma ra’ayinsu ko da kuwa abokin kawancensu ne.

8

Amma har yanzu dai babu wata amsa mai gamsarwa kan cewa: “Me yasa aka fara wannan yaƙin?” kuma “Me yasa har yanzu ba a iya bude mashigar Hormuz da karfin soja ba?”

9

A gefe guda kuma, har kullum Fadar White House kamar Tel Aviv, suna kokarin gamsar da mutanensu kan cewa an samu manyan nasarori ta hanyar kashe manyan jami’an Iran, wanda shi ma mutane da yawa suna ra’ayi sabanin hakan.

10

Misali, an yi zaton cewa kashe kwamandan rundunar sojojin ruwan kasar Janar Tangsiri, zai zama wata dama ta bude Hormuz, Amma kuma sai lamarin ya zo akasin hakan, ta yadda masu amfani da shafukan sada zumunta a Iran suke mayar da Magana da cewa: Ga dukkanin alamu dai Makullin mashigar Hormuz ya bace.